Gidauniyar Nafisa Abdullahi Za Ta Shirya Taron Tallafawa Mabukata

Gidauniyar Shahararriyar jarumar Kannywood, Nafisa Abdullahi, mai suna (Love Laugh Foundation) za ta shirya wani kasaitaccen bikin domin tara kudaden da za a rika tallafawa gajiyayyu a fadin kasar nan.


Taron wanda za a yi a jihar Kaduna, zai samu halartar manyan hamshakan mutane daga sassan kasar nan, wadanda za su bada nasu tallafin domin ganin Gidauniyar ta taimakawa mutanen da suke bukatar taimako.

Manufar wannan gidauniya ita ce tsamo al’umma daga kangin talaucin da suke fama da shi, musamman ‘yan gudun hijra, ta hanyar raba masu kayan abinci, tallafin karatu da sauran su.
A baya bayan nan, Gidauniyar ta kai ziyara kauyen Gurguzu a jihar Kaduna, inda ta tallafawa al’umma garin da abinci, nau’in shinkafa, taliya, makaroni, man kuli da sauran su.

Tuni dai shirye-shirye sun yi nisa wajen gudanar da wannan gagarumin taro, wanda za a yi a karshen watan nan na Nuwamba.

Comments