Yadda Kungiyar Bollywood Ke Tallafawa Gajiyayyu

Hadakar kungiyar masoya kallon finafinan Indiya a Nijeriya, (Bollywood Fans Nigeria) kungiya ce da ta kafu don sadar da zumuncin tsakanin mutanen da suke da sha’awar kallon finafinan Indiya a duniya.
Manufar wannan kungiya ita ce samar da hadin kai tsakanin al’umma, taimakon juna, sada zumunci da sauran su. Kasancewar mun taso mun ga yadda a shekarun baya, bata gari suna amfani da soyayyar jaruman finafinan Indiya suna hada husuma, fadace-fadace da hargitsi, wanda yanzu mun kawar da shi daga cikin al’umma.

Bollywood Fans Nigeria tana dauke da membobi daga sassa daban-daban na kasar nan, akwai Furofesoshi, Daktoci, Manyan ‘Yan Kasuwa, Ma’aikatan Gwamnati, ‘Yan Siyasa, Dalibai, ‘Yan Jarida da sauran su a cikin wannan kungiya. Shi ya sa ma wasu kafafen sadarwa suka baiwa kungiyar damar yada shirye-shiryenta. Kamar su Freedom Radio, Dala FM, Express Radio, Rahma Radio, RayPower FM, AIT, RayuwaTV da LEAERSHIP Hausa.


An kafa wannan kungiya tun kusan shekarar 2009, ta yi aikace-aikace na alheri daidai gwargwado, da suka hada da ziyartar gidan marayu, sansanin ‘yan gudun hijra, duba marasa lafiya da hada auratayya a tsakanin mambobin ta dacdai sauran su.

Kungiyar mai shelkwata a Kano tana da tsarin shugabanci mai kyau, kasancewar tana da membobi sama da dubu 100 a fadin kasar nan.

Masana harkar finafinan Indiya, sun yi tunanin kafa wannan kungiya ne domin ganin an kawar da mugayen halaye da wasu ka iya koya a fim, inda ake sharhi da fashin bakin kan ma’ana da kuma yadda ya kamata a fahimci shi kansa sakon da fim din ke dauke da shi.


A wannan kungiya, ana kokarin nuna wa matasa illar shiga munanen dabi’u, wadanda ka iya lalalata rayuwarsu, tana kuma bayyanawa mabiyanta irin kalmomi da abubuwan da ba su dace da addininmu ba da kuma al'adar mu. Har ila yau, tana amfani da dan abinda take tarawa wajen taimakon kai da kai, wajen idan dayan mu zai yi aure, ko an yi masa haihuwa, cigaban karatun sa ko rashin lafiya da dai sauran su.

Comments