Idan ana batun zuwa da wak’ok’i masu dad’i
a cikin finafinan Hausa, hak’ik’a kamfanin FKD shi ne kan gaba wajen ganin ya zo
da dad’ad’an wak’ok’in masu sanyaya zuciyar mai sauraro.
Kamfanin FKD ya yi k’aurin suna ta
wannan bangaren tun shekaru da dama da suka gabata. Domin sun fitar da wak’ok’i
wad’anda har yau d’in nan an kasa mantawa da su irinsu: Mujadala, Fil’Azal, Sai
Wata Rana, Madubin Dubawa, Adamsy, Sirrin Da Ke Raina, Halacci Halwa da kuma
baya bayan nan Gamun Nan Dai.
Wannan karon kamfanin ya sake zuwa da
wani salon na daban, wanda za a iya cewa shi ne irinsa na farko a cikin wani
sabon mai suna MANSOOR. Wak’ok’in fim din; Abin Da Yake Raina, Zan Rayu Da Ke,
Makullin Zuciya, Macukule, Jirgin So Zai Tashi da Ya Mansoor Na, tuni sun hau kan
k’adamin zamowa shahararru da za su dad’e a kunnunwa masoya.
Hak’ik’a Umar M Shareef, Abdul D. One, Murja
Baba, Maryam Fantimoti, da Khairat Abdullahi da suka bada muryoyinsu wajen rera
wad’annan wak’ok’i na mad’aukakiyar soyayya sun taka rawar gani. Da ma me ake
tsammani daga wurin mutanen da suke da tarin basirar wajen sarrafa murya don yi
wak’ar soyayya? Bari mu dan kalli wak’ok’in don yi bayani a kansu…
Abdul D. One (Marubucin Wak’a kuma Mai
Rerawa), ya yi amfani da muryarsa wajen rera wak’ar ‘Abin Da Yake Raina’ da a
yanzu samari da ‘yan mata ke yin guzurinta don farantawa juna rai. Tabbas dad’in
wak’ar ya kai matsayin da idan mutum ya kunna sai dai ya yi ta ji ba tare da ya
canja wata ba, saboda muryarsa tana da dad’in sauraro. Maryam Fantimoti, ita ma
ba a bar ta a baya ba, domin wak’ar da ta rera ‘Ya Mansoor Na’ tuni ta shiga
sahun shahararrun wak’ok’i ababen saurare.
‘Macukule,’ duk da ba irin wak’ok’in da
Umar ya saba yi ba ne, amma ya yi matukar k’ok’ari tun daga farkonta har k’arshe.
Babu wani sabon abu a cikinta, amma tsarin kid’anta ya yi matuk’ar dad’i. Har
ila yau, lafuzan da aka yi amfani da su sun tsaru tsaf, ta yadda za a
nishadantar da mai sauraro. Hakika idan wak’ar ta samu talla sosai, za ta zamo
d’aya tamkar da dubu a wurin masoya sauraron wak’a.
Fitar wak’ar ‘Zan Rayu Da Ke’ ya sauya
salon album d’in gaba d’aya, domin Umar M. Shareef ya k’ara nuna wa duniya
cewar indai bangaren wak’ar soyayya ne to da shi da na biyu. Duk wani masoyi,
ko masoyiya, zai so a ce shi ake rerawa wannan wak’a. Tuni ya sanya hatta
manyan jaruman a Kannywood da sauran mutane rera wak’a suna d’ora ta a
shafukansu na Instagram, yayin da jarumi Ali Nuhu ke bayyana farin cikinsa da
zarar sun yin hakan.
‘Jirgin So Zaya Tashi’ wadda Umar suka
rera da Murja Baba ta yi dad’i matuka, hakan yana k’ara bayyana basirar mawak’in
a fili. Kid’an ya tsaru matuka, zubin tsarin zantukan da aka yi amfani da abun
burgewa ne. Kai da nemi wak’ar kawai ka saurara.
‘Makullin Zuciyata’ irin wak’ok’in nan
ne da idan mutum ya fara saurara shi kenan sun shiga jikinsa, batun dainawa ma
sam bai taso ba. Wak’a ce da ke bayyana irin yadda masoyi ya kamu da son
masoyiyarsa, da kuma irin fatan da yake da shi na ganin ta karbi soyayyarsa da
hannun biyu.
Wad’annan su ne wak’ok’in da fim MANSOOR
yake d’auke da su, saboda haka ku saurara domin nishandatuwa da kalaman da suke
ciki.
Labari: Ali Nuhu
Tsarawa: Jamil Nafseen
Rubutawa Wak'a: Umar M Shareef, Abdul D One
Rerawa: Umar M. Shareef, Abdul D. One, Maryam Fantimoti, Murja Baba da Khairat Abdullahi.
Koyar Da Rawa: Ali Nuhu
Shiryawa: Nazir Dan Hajiya
Bada Umarni: Ali Nuhu
Tabbas maganarka hakane, kuma har a gobe babu wani kamfanin da zai gwada ma FKD irin wannan gagarumin aiki. Fatana Allah yakara daukaka wannan kamfani yakara wa sarki Ali nuhu lafiya da nisan kwana
ReplyDelete