Adam A. Zango Ya Kaddamar Da Rigar Sabon Fim Dinsa GWASKA

Shaharrane jarumin finafinan Hausa, Adam Abdullahi Zango, ya kaddamar da rantsattsiyar riga ga masoyansa mai dauke da sunan sabon fim dinsa GWASKA da yanzu haka ake dakon fitowarsa.


Ita dai wannan riga, an yi ta kala-kala yadda za ta dace da bukatar masu bukata. Sa’anna an sanya ta a farashi mai rahusa, watau naira dubu 10.

Kwanakin baya aka saka gasa ta wakar wannan kasaitaccen fim, wanda tuni jarumin ya bayyana a shafinsa na Instagram kan yadda ta kaya, inda ake sa ran za a bayyana wadanda suka lashe gasar a ranar 29 ga watan Yulin 2017 a birnin Kanon Dabo.

Zuwa yanzu dai, babu wani fim da ake tsumayin gani kamar Gwaska, musamman da yake an kalli na farko, shi ya sa mutane suka matsu su ga fitowar ci gabansa.


Rahotanni sun nuna cewa, shi wannan fim ba a taba yin irinsa ba, idan aka kwatanta da irin sidaddabarun da aka yi a cikinsa.

Comments