Dubunnan Mutane Sun Halarci Taron Tantance Jaruman Shirin Wasan Kwaikwayon ‘GISHIRIN RAYUWA’

….Shirin Na Dauke Da Darasi Kan Muhimmancin Ilmi, Cewar Dakta Sarari

Shugaban Kamfanin Sarari Klassique wanda yanzu haka suka shirya domin kaddamar da wani gagarumin fim mai suna ‘GISHIRIN RAYUWA’ ya bayyana cewar shirin wasan kwaikwayon yana dauke da darussa da suka shafi muhimmancin ilmi a cikin al’umma da kuma yadda iyaye musamman maza za su rika kula da iyalansu ta fuskar ba su ilmin da zai amfane su a rayuwa.

Alkalan yayin tantancewa

Dakta Sarari ya yi wannan batu ne bayan kammala taron tantance jaruman da za su fito a cikin wannan shiri, wanda ya samu halartar dubunnan mutane, matasa maza da mata, daga sassa daban-daban na kasar nan da ma kasashen ketare.

Daktan ya ce: “Hakika mun samu nasara karon farko, domin mutanen da suka halarci wannan tantancewa sun ba mu mamaki matuka da gaske, wannan ya kara nuna cewar lallai akwai masu sha’awar harkar nan dama ce kawai ba su samu ba.
“Tsarin tantancewa da muka bullo da shi tabbas kwalliya ta biya kudin sabulu, domin yanzu mutane za su iya samun damar shiga fim ba tare da wani ya daure masu gindi ba, ko kuma irin abin da ake cewa ‘mai uwa a gindi murhu’.

Wani sashe na mahalarta tantancewar
“Mun samu baki har daga Kudancin kasar nan; Legas, Edo, Benin da sauran su. Akwai ‘wadanda suka yi tattaki daga kasar Nijar ma. Akwai wani rol wanda mutum daya kawai ake bukata, amma sama da mutum 200 ne suka yi rajistar shiga.” In ji shi.

Sarari ya kara da cewar, hatta tsarin kasuwancin fim din na daban ne, domin za a yi amfani da matakai daban-daban domin tabbatar da ganin shirin ya shiga lungu da sako na sassan kasashen Afrika.

Wasu matasa a wurin tantancewar
Da yake amsa tambaya kan makasudin shirya wannan fim ta hanyar barkwanci, Dakta Sarari ya ce, “Dole idan kana son koyawa al’umma wani darasi, to akwai bukatar bin hanyar da za ta yi saurin kai hankalinsu gare ka. Kuma kasancewar a wannan yanayi da ake ciki mutane suna fama da matsaloli kala-kala, idan aka saka barkwanci zai taimaka kwarai wajen ragewa mutane radadi tun da idan suka kalla za su samu nishadi. Shi ya sa muka nemo marubuta a kalla bakwai, wanda a karshe guda uku suka shafe tsawo watan takwas suna tsara labarin yadda zai gamsar da mutane.” A cewarsa.

Alasan Kwalle na yi su Isyaku Jalingo bayani
Shi da wannan kasaitaccen shiri zai samu bada umarni daga shahararren darakta, Falalu A. Dorayi. Zuwa hada rahoto, kamfani Sarari Klassique ba su bayyana jaruman da suka yi nasara zamowa gwaraza a wannan tantancewa ba.

Comments