ZA A GUDANAR TANTANCE JARUMAN DA ZA SU FITO A FIM DIN 'GISHIRIN RAYUWA'

A yunkurin da ake yi na kara fadada harkokin finafinan Hausa, kamfanin Sarari Klassique zai fara tantancen sabbin jaruman da za su fito a cikin sabon shirin fim dinsa da za a fara dauka nan ba da jimawa ba.



Shirin mai suna "GISHIRIN RAYUWA" zai maida hankali ne fannin ilimantarwa da nishadantarwa da fadakarwa, kuma zai bambanta da yadda aka saba shirya sauran fina-finai.
Yanzu haka dai an bude kofa ga duk mai sha'awar shiga ko fitowa a cikin sabon shirin wasan kwaikwayon. Duk mai sha'awa zai je kai tsaye ayi masa gwaji domin tantancewa kamar haka:-

A Jihar Kano
Za'a yi taron tantance yan wasan ne:-
A Ranar Asabar da Lahadi, 22 da 23/07/2017
Waje: Dankin Taro Na Mumbayya House dake Gwammaja Kano.
Lokaci: Da Karfe 9:00 na safe
Domin karin bayani sai a tuntubi lambar waya 0703 883 8890

A Jos
Za'a yi taron tantance yan wasan ne kamar haka:-
A ranar Asabar da Lahadi 29 da 30/07/2017
Waje: Mega Park dake kan titin Bauchi, Bauchi ring road, Jos
Lokaci: Da karfe 9:00 na safe

Marubutan shirin (Writers)
Nazir Adam Salihi
Nasir Nid
Nazir Alknawi

Shiryawa (Producer)
Ahmed Muhammed Sarari

Bada umurni (Director)
Falalu Dorayi

Kamfanin SKM tare da hadin guiwar Kannywood Entertainment ne suka dauki nauyin shirin.

Domin karin bayani sai a tuntubi:
Lambar waya 07038838890

Ko a ziyarci adreshinmu na yanar gizo a www.sarariklassique.com
Rariya zata cigaba da kawo maku rahoton yadda ta kaya a wajen tantancewar. Allah yaba mai rabo sa'a

Comments