LAILA ADAM: Daban Da Sauran Finafinai

Famili Investment Nig. Int, Kamfanin da ya samu sahalewar hukumar ba da lasisin Kamfanoni ta ƙasa, kuma yana ɗaya daga cikin Kamfanonin da suke samar da ingantattun fina-finan Hausa don amfanin ‘Yan jama’a maza da mata.
Ga duk mai bibiyar harkokin masana’antar shirya fina-finan Hausa wato tsangayar Kannywood, ya kwana da sanin samun sabon canji duba da yadda sauran masana’antun samar da fina-finai na duniya suke a kan tsari na ci gaba a ko da yaushe, don haka muka ga bai dace muma a bar mu a baya ba.



To Alhamdullilah duk wanda ya ga Fim ɗin ya san babu shakka ya zo da wani sabon salo da duk wanda  ya kalli irin samfurin fina-finan da ake samarwa a yanzu zai ga wannan fim ya zo da abubuwa na zamani don ci gaba sosai.
Kamar yadda Kamfanin Famli Investment Nigeria International suka shirya wannan sabon fim mai suna Laila Adam, idan masu kallo za su tara hankalinsu su yi masa kallon tsaf za su ga yana ɗauke da ɗumbin darusa na rayuwa, da aka tanada saboda faɗakar da al’umma.

Fim ɗin ya samu aiki mai inganci sosai, kama daga tsara labarin da wurin ɗaukar shirin, duk wuri ne mai mai ƙayatarwa, labarin fim ɗin ya samu tantancewar manyan malaman jami’a da suka tace shi har sau uku don ya gamsar da al’umma kamar sauran fina-finan ƙasashen waje, ba tare da ya samu wata naƙasu ba.

Shi dai wannan fim ɗin yana da darusa masu matuƙar alfamnu ga al’umma, tunda dama manufar ko wane fim kenan, an gina wannan fim akan rayuwar zamantakewar rayuwar aure, ƙarya, rashin bincike akan abin da mutum bai da masaniya, amma ka ga mutum ya dage akan abin da yake ganin shi ne dai-dai.
Wannan fim ɗin dai gaskiya sai in har mutum ya ganshi gani na nutsuwa sannan zai san an baje kwakwalwa sosai don al’umma su san fim ɗin Laila Adam daban ne da sauran fina-finan Kannywood.



Ya samu manyan ma’aikata, tun daga labari, jarumai, masu bajinta, ƙwararru a fim, har zuwa kan mai ba da umarni.
Wanda ya tsara labarin fim ɗin shi ne Ibrahim Birniwa, sannan Sani mai Iyali ya ɗauki nauyin fim ɗin, sai Fitattacen Darakta kuma ƙwararre Ali Gumzak ya ba da umarni.
Manyan jarumai da suka taka rawa a cikin shirin sun haɗa da fitattun jarumai daga maza wato Ali Nuhu, Sadiƙ Sani Sadiƙ. Daga ɓangaren mata kuma akwai su Aisha Aliyu Tsamiya, Hafsat Idris da sauransu.

Wani abin burgewa game da wannan fim na Laila Adam shi ne, waƙoƙin cikin fim ɗin sai wanda ya ji su, domin gogaggun mawaƙa a wannan tsangaya ta Kannywood wato Nazifi Asnanic da Nura M. Inuwa.

Sani mai Iyali mashiryin  shirin fim ɗin, ya yi ƙarin haske in da ya yi kira ga abokan harkar su, wato sauran masu shirya fina-finai, da su riƙa daurewa suna kai wa Malamai suna duba labarin fim ɗinsu tun kafin fara aikin, sannan kuma a tabbata fim ɗin ya ba da ma’na yadda su kansu masu kallo za su gamsu da aikin da ke cikin Fim ɗin.

Kazalika yayi kira ga Gwamnati da Hukumomi da su riƙa tallafa wa masu, don su ƙara samun ƙwarin ƙwiwar gudanar da harkar ta su, kamar yadda sauran ƙasashen duniya ke yi.  “Haka suma masu kuɗinmu muna gayyatarsu da su riƙa zuba hannun a harkar jari don samun ci gaba da riba mai yawa.”



Wannan fim mai suna Laila Adam da zai fito nan ba da daɗewa ba, an kashe mashi maƙudan kuɗi sama da Naira Miliyan 10. Kuma muna ƙara bai wa jama’a haƙuri waɗanda suke sauraron fitowarsa, da su ƙara haƙuri a bi komai sannu in sha Allahu yana nan tafe. Fatanmu dai shi ne, masoyanmu ku taya mu da addu’a, domin addu’arku tana da matuƙar muhimmaci.


"A ƙarshe ina addu’ar Allah Ya bamu dacewa ya rabamu da duniya lafiya, ya bamu lafiya da zama lafiya a garinmu da ma ƙasa baki ɗaya amin.”

Comments