Kwankwaso Movies, Kamfani ne da ya samu
sahalewar hukumar ba da lasisin Kamfanoni ta ƙasa, kuma yana ɗaya daga cikin
Kamfanonin da suke samar da ingantattun fina-finan Hausa don amfanin jama’a
maza da mata.
Ga duk mai bibiyar harkokin masana’antar
shirya fina-finan Hausa wato tsangayar Kannywood, ya kwana da sanin samun sabon
canji da ake kokarin samarwa duba da yadda sauran masana’antun samar da
fina-finai na duniya suke a kan tsari na ci gaba a ko da yaushe, don haka wasu
daraktocin ke ganin bai dace muma a bar mu a baya ba.
Fim din BA KAMA, Fim ne da ya zo da wani
sabon salo da duk wanda ya kalli irin samfurin fina-finan da ake samarwa
a yanzu zai ga wannan fim ya zo da abubuwa na zamani don ci gaba sosai.
Kamar yadda Kamfanin Kwankwaso Movies suka
shirya wannan sabon fim mai suna Ba Kama, idan masu kallo za su tara hankalinsu
su yi masa tallansa kallon tsaf za su ga yana ɗauke da ɗumbin darusa na rayuwa,
da aka tanada saboda faɗakar da al’umma.
Fim ɗin ya samu aiki mai inganci sosai,
kama daga tsara labarin da wurin ɗaukar shirin, duk wuri ne mai mai ƙayatarwa, har
ila yau, idan aka ce ba a taba yin fim irin sa ba. Babu shakka mutane za su
gamsu, domin a duniyar finafinan Hausa, ba a taba fitar da salon irin wannan
ba. Bugu da kari, labarin fim ɗin ya samu tantancewar manyan malaman jami’a da
suka tace shi har sau uku don ya gamsar da al’umma kamar sauran fina-finan ƙasashen
waje, ba tare da ya samu wata naƙasu ba.
Shi dai wannan fim ɗin yana da darusa masu
matuƙar alfamnu ga al’umma, musamman a duniyar ta yanzu wadda take tafiyar
karkashin inuwar Kimiyya da Fasaha.
Kusan kowa yana sane da bala’in barayin
zaune, wadanda ke amfani da na’ura mai kwakwalwa su yi sata, to wannan fim an
yi amfani da basira, tunani, kayan aiki irin na zamani domin a gabatarwa da
masu kallo shi, ko ba komai, canji da ake fatan ganin an samu tun tale-tale, an
samar da shi yanzu.
Wannan fim ɗin dai gaskiya sai in har
mutum ya ganshi gani na nutsuwa sannan zai san an baje kwakwalwa sosai don
al’umma su san fim ɗin Ba Kama daban ne da sauran fina-finan Kannywood.
Ya samu manyan ma’aikata, tun daga labari,
jarumai, masu bajinta, ƙwararru a fim, har zuwa kan mai ba da umarni.
Produced by Nazir Dan Hajiya
Directed by Falalu A. Dorayi Screenplay Ibrahim Birniwa Cast Adam A. Zango Hadiza Aliyu Gabon Rahma Sadau Fati Washa Aminu shAriff Momo Isah Ferozkhan
Comments
Post a Comment