Shahararren kamfanin shirya
finafinan Hausa, Maishadda Global Resources Nijeria Limited, ya shirya tsaf
domin fara haskawa al’umma fim din da aka dade ana jira, watau WUTAR KARA.
Kamar yadda shugaban kamfani kuma
furodusan fim din, Abubakar Bashir Maishadda ya shaida mana, ya ce gobe Juma’a,
za a fara nuna fim din a babbar sinima da ke Ado Bayero Mall kan titin Zoo Road
da ke birnin Kano.
Maishadda ya ce, “Wutar Kara fim ne
mai dauke nishadi, har ila yau cike da sako. Mun shirya fim din ne kan matsalar
rabon gado da take addabar mutane. Shi ya sa muke son wayar da kan al’umma ta
hanyar nishadi. Su karu, a lokacin guda kuma zuciyoyinsu su fari.
Ya kara da cewar, shirin Wutar Kara
na cikin finafinan da kamfaninsa yake alfahari da su, domin an zage jiki sosai
wurin gudanar da aikinsa domin dai ya kayatar da ‘yan kallo.
“Kamfaninmu kullum burinsu ya
shirya fim mai dauke da sako, sannan mu nishadantar da al’umma. Finafinanmu na
baya sun samu yabo matuka da gaske daga wurin al’umma, shi ya sa ba ma yi kasa
a gwiwa wajen nutsuwa tare da yin bincike don ganin wace mas’alah ce mutane ke
bukatar a yi musu fim a kai.
“Duk da cewa fim din Wutar Kara
wasan kwaikwayo ne na barkwacin, amma mun yi matukar kokari wajen gabatar da
sakon matsalar rabon gado da ke damun al’umma. Saboda haka ina kira ga masu
sha’awar kallon finafinan Hausa da su zo a mu hadu a Shorprite, Ado Bayero Mall
domin mu kalli wannan fim tare da su.” In ji Maishadda.
Za a iya cewa Kannywood ta dade ba
ta shirya fim wanda yake dauke da manyan jarumai kamar Wutar Kara. Har ila yau,
kwararru ne suka taru wuri guda domin shirya shi yadda zai yi wa ‘yan kallo
armashi.
Wutar Kara ya samu bada umarni daga
kwararren darakta, Yaseen Auwal, yayin da Abubakar Maishadda ya rufa masa baya
wajen shiryawa.
Jaruman shirin sun hada da: Ali
Nuhu, Ibrahim Mandawari, Abba El-Mustapha, Sadiq Sani Sadiq, Aminu Shariff
Momo, Maryam Yahaya, Maryam AB Yola, Salisu S Fulani, Shamsu Dan Iya, Maryam
CTV, da sauran su.
Tuni dai aka fitar da lokutan nuna
wannan fim kamar haka; 10:20am, 12:20pm, 2:20pm, 4:20pm, 5:45pm, 8pm,8:20pm.
Comments
Post a Comment